Hukumar ta ce adadin mutane da basa samun isashen abinci kuma mai gina jiki a yankin na kudancin Afika ya yi sama da kashi 10 cikin 100 daga shekearar da ta gabata.
Annobar COVID-19, da ta hadu da sauyin yanayi da kuma fadi-tashin tattalin arziki da kasashe da dama suke fama da shi, shi ne babban abin da ya haddasa karancin abincin.
Kasar Zimbabwe ce kasar da lamarin ya fi kamari, inda ake sa ran adadin mutanen da suke fama da karancin abinci zai kai miliyan 8.6 zuwa karshen wannan shekarar.
Daraktar hukumar abinci ta duniya a kudancin Afirka, Lola Castro, ta ce yankin ya fi fuskantar kalu-balen sauyin yanayi.
“Za mu fuskanci matakai na karancin abinci irin wanda ba mu taba gani ba a shekaru da dama a larduna 13 na gundumomi 16," Inji Casto.
“Muna da kwararan dalilai da muka sani sosai, kuma suna da alaka da sauyin yanayi da fari, da ambaliyar ruwa ko matsananciyar guguwa a cewar Casto.
Ta ce COVID-19 da coronavirus ke hadasawa, tana daga cikin matsala ta gaggawa da ke illata al’umma sosai musamman talakawa a nahiyar.
Ta kara da cewa zaman kulle, sanadiyar cutar ya haddasa rashin aikin yi a tsakanin al’umma da yawa, ya haifar da rashin abinci.
Facebook Forum