Jami'an bincike da aikin gaggawa a Rasha, sun bincike wani fili mai cike da kankara a yau litinin a bayan garin Birnin Moscow, inda suke neman barbashin wani jirgin sama da ya fado a jiya wanda ya kashe mutane 71 da ma'aikatan jirgin da kuma kanana yara uku.
Pasinjojin guda 65 ne suke cikin jirgin wadanda shekarun su ya kama daga shekaru 5 zuwa 79 ne a cewar wata takarda da m'aikatar aikin bada agajin gaggawa ta Russia ta fitar, amman bata bayyana asalin kasashen mutanen ba.
Ma'aikatar ta bayyana cewa fiye da mutane 400 da motoci 70 aka aika wajen da hadarin ya auku, kuma shugaban kasar Vladmir Putin ya bayaar da umarni da a kafa kwamiti na musamman domin binciken abinda yai sanadiyyar hadarin samfurin Antonov mai lamba AN-148 jim kadan bayan tashin shi.
Ana zargin tana yiyuwa ajizancin dan adam, ko matsalar inji, da kuma matsalar yanayi na daga cikin dalilai da ake zargin suka haddasa wannan hadari a cewar hukumar binciken Rasha, kuma basu fadi ayyukan ta'adda a cikin abubuwan da ake zargi ba
Facebook Forum