Har yau ana ci gaba da samun saukar ruwan sama a sassan kasar lamarin da masana ke alakantawa da canjin yanayin da ake fama da shi a kasashen Sahel, yankin da zaizayar kasa da gurgusowar hamada ke kara kamari.
A yayin bitar da hukumomi ke yi lokaci zuwa lokaci don sanar da al’umma halin da ake ciki a sassan kasa dangane da tafiyar damanar bana, ma’aikatar agajin gaggawa ta kasa wato Direction de la Protection Civile ta ce mutane 1, 176, 528 ne suka rasa muhallansu sanadiyar ambaliya.
Iftila’in ya kuma hallaka mutane 339 yayin da wasu 383 suka ji rauni ba’idin asarar dimbin dukiyoyin da suka hada da dabobi 22, 476 da suka mutu hade da salwantar abincin da yawansa ya kai tan 25, 695.
A baya hukumomi sun sanar cewa sun tallafa wa irin wadanan mutane da ton ton da dama na kayan abinci. Ganin yadda matsalar ta yi kamari ya sa masani kan dabarun ayyukan noma da kiwo Dr. Haboubacar Manzo shawartar ma’aikatan game da bukatar karfafa matakai.
Matsalar ta fi kamari a jihar Maradi inda abin ya haddasa mutuwar mutane 111, sai jihar Tahoua inda aka sami asarar rayukan mutane 99 sannan Jihar Zinder mai mutuwar mutane 65 sannan Dosso da Tilabery da Diffa a cewar ma’aikatar agaji ta kasa.
Watanni a kalla 3 da rabi ne aka kwashe ana tafka ruwan sama kamar da bakin kwarya a wani al’amarin da wasu ke cewa marabin a ga faruwar makamancinsa a Nijar an kai shekaru kusan 50. Abinda ke zama wata manuniyar dake fayyace girman illolin canjin yanayi a yau.
Haka kuma hanyoyin zirga-zirgar motoci da dama ne ruwa ya lalata a tsakiyar wannan damina lamarin da ya shafi harakokin sufuri a tsakanin birnin Yamai da sauran jihohi kafin daga bisani hukumomi su dauki mataki a yayin da mutanen da gidajensu suka ruguje sanadiyar wannan bala’i ke ci gaba da samun mafaka a makarantun boko, lamarin da gwamnatin kasar ta ayyana a matsayin dalilin dage ranar bude makarantu daga 1 ga watan Oktoba zuwa ranar 28 ga watan.
Ga rahoton wakilin Muryar Amurka a Yamai Souley Moumouni Barma cikin sauti:
Dandalin Mu Tattauna