Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Muryar Amurka tayi tir da gitta zangon watsa shirye shiryenta


Darektan Murayar Amurka David Ensor
Darektan Murayar Amurka David Ensor
Gidan Rediyon Muryar Amurka ya nuna bacin rai game da gitta masa zongon yada shirye-shiryen Turanci a kasar China.

Babban Darektan Gidan Rediyon Muryar Amurka David Ensor ya yi Allah wadai da gittawar baya-bayan nan, ya kuma ce kafar yada labaran ta gwamnatin Amurka na aiki da kwararru don gano takamaimai daga inda ake gittawar. Ya ce yada bayanai ba tare da hani ba wata dama ce ta kasa da kasa kuma Muryar Amurka za ta cigaba da bayar da bayanai na gaskiya kuma wadanda babu son kai ciki ta kafar da ka iya zuwa ga masu saurare a wuraren da ake da takunkumin yada bayanai.

Gidan Rediyon na Muryar Amurka da gwamnati ke daukar nauyinsa ba shi ne kadai matsalar gittawar ke shafa ba. Gidan Rediyon BBC ma ya fadi a wannan satin cewa ana ta gitta shirye-shiryen sa na Turanci na gajeran zango a China.

Gidan Rediyon BBC ya ce koda yake ba shi yiwuwa a san wanda ke gitta masa zangon yada shirye-shiryen, tsananinsa da kuma irin salon gudanar da shi ya yi kama da yadda kasa irin China ke yi.
  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG