Takaddama tsakanin Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben shekara ta 2015 da gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike, ta soma ne tun daga lokacin shirye-shiryen gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyar a zaben na 2015.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya soma ne bayan da aka yi zargin cewa Wike na aiki ta karkashin kasa har ma da bayyane, domin samar da dama ga gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal, don ya sami tikitin jam’iyyar na tsayawa takarar shugaban kasa a lokacin, har ma da zabe mai zuwa na shekarar 2023.
Wannan ya haifarda rashin jituwa a tsakanin manyan jiga-jigan biyu, ya kuma haifar da wata takaddama tsakanin Wike din da shugaban jam’iyyar ta PDP Uche Secondus, wanda ake ganin yana goyon bayan bangaren Atiku.
To sai dai kuma kusoshin PDP din sun nuna alamun dinke barakar da ke tsakaninsu, tare kuma da bayyana kudurinsu na yin aiki tare domin ci gaban jam’iyyar, a wata ganawa da suka yi a birnin Fatakwal na jihar Rivers.
Wata majiya kwakkwara ta bayyana cewa an jiyo Neysom Wike yana cewa “idan har Atiku Abubakar na iya zamantakewa cikin lumana da hadin kai da matansa 3, Bahaushiya, Bayarabiya da ‘yar kabilar Igbo, to kuwa lalle zai iya hada kan Najeriya.”
Wannan lamari ya kuma faranta ran ‘yan jam’iyyar ta PDP da dama, musamman wadan da ke cikin alhini da fargaba na rasa wasu gwamnoni da kusoshin jam’iyyar da suke sauya sheka zuwa APC, a yayin da aka tunkari babban zaben shekarar 2023.