A wani taro da suka gudanar a Bauchi, gwamnonin na PDP sun kuma kalubalanci yunkurin tilasta bin tsarin zaben fitar da gwani a matsayin hanyar tsayar da ‘yan takara ga dukan jam’iyyun siyasa.
A wata sanarwa da suka fitar bayan taron na Bauchi, gwamnonin na PDP sun bayyana cewa tsarin tilasta zaben fitar da gwani na kai tsaye kamar yadda yake a kudurin yin gyara ga dokar zabe, cike yake da ayukan magudi da aringizo.
To sai dai sun ba da shawarar cewa kamata yayi a baiwa jam’iyyun siyasa damar su yanke hukunci akan ko su gudanar da zaben fidda gwani kai tsaye ko ta sasantawa a matsayin siyasar cikin gida ta jam’iyyu.
Sanarwar ta ce “gwamnonin sun yi amanna da samun sahihi kum ingantaccen zabe a Najeriya, akan haka suka yi kira ga majalisar dokoki ta tarayya da ta karfafa amincewa da tsarin tattarawa da aikewa da sakamakon zabe ta na’ura a tsarin zaben kasar.”
Haka kuma sun bukaci hukumar zabe ta INEC da kundin tsarin mulki ya dorawa alhakin gudanar da zabe, da ta yi amfani da dukan hanyoyin fasahar zamani da suka saukaka, wadanda ake bukata wajen tabbatar da kowace kuri’a da dan Najeriya ya kada za ta yi tasiri a zabe.
Gwamnonin sun kuma yi kira ga hukumomin watsa labarai da ma na sadarwa kamar NCC, USPF da sauran kamfanonin sadarwa, da su tabbatar da baiwa kowa dama ta bai daya musamman a yankunan karkara, domin samun ayuka da bayanai tun kafin gudanar da babban zaben kasar na shekarar 2023.
Haka kuma sun yi Allah wadai da abin da suka kira “dabarun tilastawa wasu gwamnonin PDP da wasu kusoshin jam’iyyar ta adawa domin su koma APC.
Batun yin gyara ga dokar zabe da ya kumshi amfani da na'ura wajen tattara sakamakon zabe, da kuma sha'anin zaben fidda 'yan takarar jam'iyyu da yanzu haka ke gaban majalisar dokokin tarayya, na ci gaba da haifar da cece-kuce da ra'ayoyi mabambanta.
Ko a kwanakin baya ma wasu kungiyoyin rajin kare dimokaradiyya a Najeriya, sun fito da kakkausar murya suka nuna rashin goyon bayansu akan abinda suka kira "yunkurin wasu 'yan majalisar dokoki na dawwama kan kujerunsu ta hanyar gyara ga dokar zabe ta kasa."