Hukumar ta kai samamen ne a cikin gidajen wani mutum mai suna Ugochukwu Nsofor Chukwukabia dake rukunin gidajen Victoria Garden City a anguwan lekki dake Legas a lokacin wani samame da jami’an hukumar suka kai a ranar Juma'a.
Wata sanarwa da kakakin hukumar Femi Baba Femi ya aikewa ‘yan jaridu tace an sami kwayoyin ne a wasu katan- katan na muggan kwayoyi sanfarin Tramadol da yawan sa ya kai fiye da miliyan 13 a birnin Legas.
Hukumar tace ta kama Mr Ugochukwu dake zama shugaban kanfanin motoci na autonation, wanda dama ta dade tana bibiyar sa, bisa zargin mu’amula da muggan kwayoyi a Najeriya.
Wannan kame da hukumar ta NDLEA tayi yazo ne wata biyu bayan ta kama wani mai hadahadar muggan kwayoyin Chris Emeka Nzewi da abokin aikin sa a bisa zargin sarrafa kwayoyin methamphetamine duk dai a anguwan rukunin gidajen na Victoria Garden City.
Ko a makon da ya gabata sai da hukumar ta kone hodar iblis na biliyoyin naira data kama a birnin na Legas.
Tuni shugaban hukumar ya yaba da kokarin da jami'an hukumar ke yi na kama manyan masu safaran muggan kwayoyi a Najeriya, tare kuma da godewa hukumomin yaki da muggan kwayoyi na Amurka bisa taimakon da suke baiwa hukumar ta NDLEA a Najeriya.