Hukumomin sun ce an samu ci gaban ne duk da irin gibin da matakin rufe iyakokin Najeriya ya janyowa asusun gwamnati a kwanakin baya.
Yayin wata zantawa da Muryar Amurka, Magatakardan kungiyar jami’an haraji, Moussa Oumarou, ya ce, biliyan 500 na cfa suka yi nasarar karbowa daga hannun talakawa da sunan haraji a bara kadai.
Hakan kuma a cewarsa, na nuni da cewa an samu ci gaba sosai idan aka kwatanta da shekarun da suka shige.
“Najeriya, babbar kasa ce mai iyaka da yawa da Nijar, duk inda ka bi za ka iya shiga Najeriya, akwai kuma hadahadar kasuwanci tsakaninmu da Najeriya, wannan hada-hada da ake yi tsakaninmu, ta rage kudaden da ke shiga baitulmalin kasa,” a cewar Oumarou.
“Abin da muke fata, gwamnatin kasar Nijar da Najeriya, su tattauna tsakaninsu domin a samu maslaha,” ya kara da cewa.
Saurari cikakkiyar hirar a nan:
Facebook Forum