Rahotanni daga jihar Zamfara na bayyana cewa rundunar sojin Najeriya na ci gaba da luguden wuta da ruwan bama-bamai kan sansanonin ‘yan bindiga a jihar Zamfara, a wani yunkuri na dakile ayukan tada kayar baya da ke neman shige makadi da rawa a jihar.
Hakan na zuwa ne kwanaki 3 bayan da aka rufe dukkan kafofin sadarwa, kasuwanni da ma wasu manyan tituna, tare kuma da takaita zirga-zirga a jihar.
Wata sanarwa da kwamishinan watsa labaran jihar ta Zamfara Ibrahim Dosara ya fitar, ta ce sojojin sama suna luguden wuta da ruwan bama-bamai ba kakkautawa daga sama kan sansanonin ‘yan bindigar, yayin da su kuma sojin kasa suke bi domin fatattakar wadanda ke neman tserewa a dajin.
Sanarwar ta ce ya zuwa yanzu sojojin sun sami tarwatsa wasu sansanonin ‘yan bindigar da suka hada da dabar shahararren jagoran ‘yan ta’adda da aka fi sani da ‘Dankarami’ a karamar hukumar mulki ta shinkafi.
A ‘yan watannin baya ne wani hoton bidiyo ya karade kafafen sada zumunta na yanar gizo, da ke nuna Dankarami tare da mabiyansa suna bikin murnar samun galaba kan sojoji a cikin daji.
Wasu rahotannin kuma sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun soma kwararowa cikin gari domin gudun tsira da rai sakamakon ruwan wutar da sojoji ke yi a sansanoninsu.
Akan haka ne gwamnatin jihar ta kafa dokar rurrufe dukkan tashohin motar da ke kan tituna, da suka hada da kan titin Kauran Namoda-Jibiya, mahadar titin Lambar Bakura, mahadar titin Anka a Kwanar Mayanchi, Garejin Mai Lena da kuma babbar kasuwar kayan abinci da na marmari da ke cikin Gusau, babban birnin jihar ta Zamfara.
Wannan da shi ne mataki na baya-bayan nan da hukumomi suka dauka na yaki da ‘yan bindigar da suka addabi al’umma da kai hare-hare, kisan jama’a da satar dabbobi da mutane domin karbar kudin fansa a jihar ta Zamfara da ma makwabtan jihohi.
Ko Kun San Irin Makaman Da Sojoji Ke Amfani Da Su Wajen Yaki Da 'Yan Bindiga A Jihar Zamfara?