Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mummunan Farin Ya Addabi Jama'a A Somaliya


Manyan jami’an gwamnatin Somaliya sun ce kusan fiye da mutane 110 ne mafi yawa cikinsu mata da yara suka mutu daga cututtukan da ke iya kamuwa dasu ta hanyar ruwa cikin awanni 48 sakamakon mummunan farin da ya addabi kasar.

Yayin da yake taron ganawa da yan jaridu a yau Asabar a Moghadishu, sabon firaministan kasar Hassan Ali Khaire ya sanar da rashin, inda ya bada cikakken adadi na gwamnati na farko, watanni bayan mummunan farin.
Firaministan yace “An sanar dani a yau cewa mutane 110 suka mutu sakamakon Farin da yake damun mu cikin awanni 48 a wasu ban garori na Somaliya , Wadanda suka hada da Bay da kuma Yankin Bakol,” ya kuma yi kira ga Yan kasar ta Somaliya da sauran Al’ummomi dake fadin duniya da su taru domin bayar da agajin gaggawa don ceton rayuka.

Kungiyar Kasa da kasa ta Masu kaura IOM a takaice na neman kimanin dalar Amurka Miliyan $24.6 domin gudanar taimakon na ceton rayuka ga daruruwan mutanen dake fuskantar barazanar Farin a Somaliya. Kungiyoyin agaji sun bada rahoton mai nuna alamun wanna yanayin da ake ciki yayi kama da yanayin da kasar ta Somaliya ta fuskanta a shekarar 2011 inda farin ya kashe mutane fiye da 250,000.

Haka kuma Kungiyoyin agajin gaggawa na Majalisar Dinkin Duniya sun bada gargadi a kwanakin baya na cewa watanni biyu ne suka rage a kare afkuwar mummunan hadarin da farin ka iya jawowa a Somaliya

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG