Daraktar gidan rediyon Muryar Amurka, Amanda Bennett ta yi jawabi kan muhimmacin 'yancin 'yan jarida a yanayi mai sarkakkiya irin na annobar cutar korona.
Ta yi jawabin ne albarkacin ranar 'yancin 'yan jarida inda ta ce:
"Suna na Amanda Bennett. Ni ce Daraktar Gidan Rediyon Muryar Amurka. Kuma Ina maku magana ne daga gida na inda, kamar akasarinku, na ke killace saboda yaduwar da Koronabairos ke yi.
Koronabairos wani al’amari ne wanda ke nuna mana abin da ya sa ‘yancin jarida ke da muhimmanci, fiye da duk yadda aka taba sani. Saboda akwai dinbin munanan labarai, da dinbin labaran karya, da dinbin labarai na rufa-rufa, ta yadda jama’a a duk sassan duniya ke dogara gare mu, don samun labarai sahihai.
Kuma saboda haka, mu ke dogara ga dukkannin gwarazan ‘yan jarida a dukkan sassan duniya, wadanda watakila ma su ke a wuraren da babu ‘yancin jarida, duk da haka su ke cigaba da turo mana hakikanin gaskiya game da cutar ta koronabairos a kasarsu."
Ga hoton bidiyon jawabin:
Facebook Forum