Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Muhimmancin Mata, Yara Wajen Wanzar Da Zaman Lafiya Da Tsaro A Duniya,


Linda Thomas-Greenfield - Wakiliyar dindindin ta Amurka a Majalisar Dinkin Duniya
Linda Thomas-Greenfield - Wakiliyar dindindin ta Amurka a Majalisar Dinkin Duniya

"Mata da matasa na da muhimmanci wajen wanzar da zaman lafiya da tsaro a duniya," a cewar Majalisar Dinkin Duniya. Lallai, idan aka jaddada daidaito tsakanin jinsi tun da ƙuruciya, “zaman lafiya, samar da tsaro na iya taimakawa wajen kange al’ummar gaba daga maimaita tsarin da kan haifar da tarnaki

WASHINGTON, D. C. - Haka zalika, tsare-tsaren da kan amfanar da mata za su taimaka wajen samar da daidaito da tsayayyiyar al'umma.

“Amurka ta daɗe da yin imani cewa, idan muka zaburad da matasa, muna zaburad da mata ne; kuma idan muka zaburad da mata, to mun zaburad da matasa; kuma idan muka zaburad da duka biyun, mun ƙarfafa dukkan al'umma; haka kuma karfafa irin waɗannan ƙungiyoyin, a cikin al'ummominsu, samar da karin aminci da kwanciyar hankali ne gare mu ba ki daya," in ji wakiliyar dindindin ta Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Linda Thomas-Greenfield.

“Abin takaici, mun kuma san cewa a yanzu, matasa, musamman ma mata, suna fama da rikice-rikice. Tashe-tashen hankula na kawo cikas ga ilimin su kuma yana rage musu sha’awar aiki, yana gusar musu gurin su a gaba. Yana takaita mu su damar shiga wuraren jama'a da tauye karfin tattalin arzikin su."

Duk da haka, "Duk da tarnakin da ake samu, mun ga matasa a duk faɗin duniya sun tashi tsaye don tunkarar wadannan ƙalubalen, kuma sun zama masu tsara makomar su," in ji Ambassador Thomas-Greenfield. "Dole ne mu yi duk abin da za mu iya don tallafawa da kuma zaburad da wadannan matasa."

“Wannan ita ce manufar da ke tattare da tsarin dabarun Amurka don kaucewa afkuwar rikici da inganta zaman lafiya, wanda ke tabbatar da goyon bayan mu ga tsarin siyasa da ya kunshi duk kan tsare tsre domin magance munanan rikice rikicen da ke wanzuwa a halin yanzu, tare da jaddada muhimmiyar rawa mai ma’ana da mata da matasa za su taka.."

Ambasada Thomas ta ce: "Tattara abubuwa mabanbanta wuri daya, da suka jibanci shiyyoyi dabam dabam, masu matukar muhimmanci da ke da alkibla ga al’umma mabanbanta a tasre tsaren zaman lafiya da tsaro, ba wai abu ne muhimmi kawai da za a aiwatar ba, ita ce hanya daya tilo da za’a tabbatar da cewa, mafitar da muka samar ta kunshi kowa, ta amfani kowa kuma ta kasance mai dorewa.," in ji Ambasada Thomas-Greenfield.

“Waɗannan ba shawarwari ba ne waɗanda wasu daga waje ke ganin ana tilasta wa ƙasashe kamar yadda wataƙila kuka ji. Wadannan shawarwari ne da matasan wadannan kasashe ke bukata kuma suke nema.”

Ambasada Thomas-Greenfield ta ce "Daga karshe, zaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa na iya samuwa ne kawai idan aka zama tsintsiya madaurin ki daya wajen bin tsare tsaren cimma wata matsaya ko yanke shawara ." "Don haka, ya zama wajibi a gare mu mu yi aiki tare don fito da dimbin baiwar da Allah ya yiwa mata da matasa, don yin aiki tare da su a yau da kuma kowace rana."

Wannan sharhi ne da ke bayyana ra’ayin Gwamnatin Amurka.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG