Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Muhimman Abubuwa Goma Game Da Tsohon Shugaban Tanzania John Magufuli


Tsohon Shugaban kasar Tanzania John Magufuli.
Tsohon Shugaban kasar Tanzania John Magufuli.

Al'ummar kasar Tanzania suna zaman makokin rasuwar shugaban kasar na biyar John Magufuli, wanda ya rasu a wani asibiti da ke birnin Dar es Salaam.

  1. Shine shugaban kasar Tanzania na biyar. Ya gaji jakaya Kikwete wanda ya yi mulki a kasar na tsawon shekaru goma- wa’adin mulki biyu.
  2. Ya zabi macen farko Samia Suluhu a matsayin mataimakiyar shugaban kasa, wadda a yanzu haka ta ke zaman shugaban kasa ta riko kafin rantsar da ita a matsayn shugaban kasa bisa tsarin mulkin kasa.
  3. Ya yi ilimi mai zurfi a fannin kimiyya, ya na da kwarewa a fannin ilimin sinadarai fannin da ya sami digirin digirgir. Ya yi karatunsa da rayuwarsa duka a kasar Tanzaniya.
  4. Ya wakilci mazabun Biharamulo ta gabas da Chato a majalisar dokokin tarayyar kasar daga inda ya tsaya takarar shugaban kasa.
  5. Ya yi minista na tsawon shekaru da dama a ma’aikatu dabam dabam.
  6. Yana daya daga cikin fitattun mutane a nahiyar Afrika da basu yarda da batun cutar Korona ba. Ya kuma ta musanta cewa akwai cutar a kasar sai bayan da wani babban sakatarensa ya mutu sakamakon kamuwa da cutar. Ya bayyana cutar Korona a matsayin :kwayar cutar ibilis da ba ta iya zama a jikin Almasihu”.
  7. An daina ganin shi a bainin jama’a tun ranar 27 ga watan Fabrairu, abinda ya sa aka yi ta rade radin cewa bashi da lafiya, batun da gwamnatin kasar ta musanta har da kama wadanda ake zargi da yayata labaran kage. Ba a sanar da rashin lafiyarsa ba sai bayan mutuwarsa.
  8. Da farkon mulkinsa an yi ta yaba kokarinsa na yaki da cin hanci da rashawa da bunkasa harkokin tattalin arziki abinda ya sa aka bashi lakabi “Bulldozer” amma daga baya aka fara zargin shi da bita da kullin siyasa.
  9. Gwamnatinsa ta rufe kafofin watsa labarai da dama, ta rika toshe hanyoyin sadarwar internet na ‘yan siyasa, da kuma kuntatawa ‘yan hamayya
  10. Ya mutu yana da shekaru 61 a duniya, yana shekarar farko a wa’adin mulkinsa na biyu. Ya rasu ya bar matarsa Janeth da ‘ya’ya biyu.

shugaban-tanzania-john-magufuli-ya-mutu

voa60-afirka-shugaba-john-magfuli-na-tanzania-ya-kalubalanci-sahihancin-wasu-magungunan-rigakafin

shugaban-tanzania-na-tababa-kan-ingancin-rigakafin-coronavirus

Karin bayani akan: Samia Suluhu Hassan, John Magufuli, da Tanzania.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG