Wannan kwamiti ne da ke kunshe da mutum 9 a karkashin jagorancin Karamin Ministan albarkatun man fetur Timpre Sylva wanda zai kula da yadda zaa aiwatar da sabuwar dokar masana'antar man fetur ta kasa wacce ake sa ran yi mata garambawul da kuma tabbatar da cewa sabbin cibiyoyi da za a kirkiro a masana'antar za su samu cikakken ikon isar da ayyukansu a karkashin sabuwar dokar wacce aka riga aka sa mata hannu.
Amma ga tsohon Mukaddashin shugaban kungiyar ma'aikatan man fetur ta Kasa Comrade Isa Tijjani ya ce indai kwamitin zai yi aiki ne akan sabuwar dokar masana'antar man fetur ta kasar ne, yana ganin akwai sauran rina a kaba.
Tijjani ya ce a wani fannin da zai ja hankali shi ne batun zuba hannun jari a masana'antar, domin sai an fayyace yadda kudin man fetur zai zama a kasa.
Komred Tijjani ya ce, idan ana so a fahimci wanan dokar, sai a baje ta a faifai kowa ya gani, sannan a ba kowa dama na yin tambayoyi in ba haka ba zai iya kawo wa kasa rudani.
Sai da ga tsohon Jami'i a ma'aikatar man fetur ta Kaduna, Dokta Kailani Mohammed yana ganin za a iya kammala aikin a cikin watanni shida kacal domin masana'antar tana da kundaye na bayanan da za a yi amfani da su wajen warware matsalolin da mutane ba su fahimta ba yana mai cewa c igaba aka samu a bangaren man fetur ta kasa.
Shugaban Ma'aikatar man fetur ta kasa Mele Kolo Kyari ya ce abu ne da 'yan Najeriya za su ga alfanunsa nan ba da jimawa ba, domin za ta samu kudaden shiga masu yawa, sannan kuma matasa za su samu ayyukan yi.
An dai baiwa kwamitin wa'adin watanni 12 na kammala aikin da Shugaba Mohammadu Buhari ya ba su.
Saurari cikakken rahaton cikin sauti: