Jiya Jumma’a birnin Minneapolis na Amurka, ya yanke shawarar hana ‘yan sanda damke wadanda ake zargi ta wuya, bayan da wani ba-Amurke bakar fata ya mutu a hannun ‘yan sanda, al’amarin da ya janyo zanga zanga ta tsawon kusan makwanni biyu.
Wakilan hukumomin birnin sun cimma matsaya da rundunar ‘yan sandan jahar Minnesota kan kawo karshen kama mutane ta wuya, tare kuma da umurtar ‘yan sanda su bada rahoton duk wani takwaran aikinsu da ya yi amfani da karfin da ya wuce kima.
(Wasu masu zanga zanga kusa da fadar White House ranar Alhamis)
Majalisar Gudanarwar Binrin Minnneapolis ta kada kuri’ar amincewa da matsayar da gagarumin rinjaye bayan da Sashin Kare Hakkin Dan Adam na jahar Minnesota ya fara binciken yiwuwar take hakkin dan kasa a wannan al’amari na mutuwar George Floyd.
Floyd ya mutu ranar 25 ga watan Mayu bayan da wani dan sanda farar fata ya dora gwiwarsa a wuyar Floyd ya danne na tsawon sama da minti takwas, yayin da Floyd ke ta rokonsa cewa bai iya numfashi, wanda wannan shi ne na baya bayan nan a yawan mutuwar Amurkawa bakaken fata a hannun ‘yan sandan fararen fata.
Facebook Forum