Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ministocin Harkokin Wajen Kasashen NATO Zasu Yi Taro Yau Akan Rasha


Babban Sakataren NATO Jens Stoltenberg
Babban Sakataren NATO Jens Stoltenberg

Zaman tankiyar da kasashen kawancen NATO da Rasha su keyi ya sa ministocin harkokin wajen kasashen yin taro na musamman akan kasar ta Rasha a birnin Brussels yau

Ministocin harkokin kasashen waje na Kungiyar Tsaro ta NATO zasu gudanar da wani taro yau juma’a a Brussel, kuma zaman tankiyar da akeyi da Rasha shine babban agendar taron.

Babban taron ko ya biyo bayan makonni ne da kasashen yammaci Turai suka yi suna zargin kasar ta Rasha da laifin anfani da guba wajen kashe wani tsohon mai liken asiri dake zaune a Birtaniya.

Haka kuma an samu Karin zaman na dar-dar da kasar taxRashalokacin da kawar ta Rasha, Syria ita ma akayi zargin ta kai hari da makami mai guba, wannan yasa Amurka Faransa da Birtaniya suka kai mata hari,sai dai wannan harin, ba kungiyar ta NATO ce ta shirya ba, shi illa kawai ta bada goyon bayan ta.

Taron na yau Jumaa dai shine zai zama irin san a karshe ababban gininna kungiyar dake Brussel kafin kungiyar da daukacin maaikatan ta su 29 da jakadun kasashen dake cikin kungiyar su koma cikin katafaren ginin nan da aka gina akan kudi har dala biliyan daya da rabi, A cikin watan yuni ne dai zasu koma cikn wannan sabon ginin.Sakatare Janar na Kungiyar Jen Stoltenberg, ya fada jiya alhamis cewa har yanzu dai babban kalubale taron zai fuskanta shine abinda ya kira mummunar tabioi irin na kasar ta Rasha.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG