Wadda ke binciken katsalandan ko kusten da Rasha tayi a zaben shugaban kasa da aka yi anan Amurka a bara. Ana sa ran Sessions zai amsa tambayoyi kan batutuwa da suka taso game da shi a makon jiya, lokacinda tsohon darektan hukumar FBI James Comey, ya bayyana a gaban kwamitin.
Sessions ya tsame hanunsa daga dukkan al’amurran da suka jibanci binciken da ma'aikatar shari'a wacce take karkashinsa take gudanarwa kan zargin take-taken na Rasha lokacin zaben, domin yana daga cikin jami'an kwamitin yakin neman zaben Trump, da suka gana da jakadan Rasha a Amurka gabannin zaben.
A cikin watan Janairu lokacinda ya bayyana domin a tantance shi zama ministan shari'a. Da yake amsa tambayar da senata Al-Franken dan Democrat mai wakilatar jahar Minnesota ya yi masa, Sessions yace bai gana da wani jami'in kasar Rasha ba a lokacin yakin neman zaben na Amurka
Facebook Forum