Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Miliyoyin Mutane Na Bukatar Agajin Gaggawa A Arewa Maso Gabashin Najeriya – Kungiyoyin Agaji


'Yan Najeriya Masu Gudun hijira a Niger
'Yan Najeriya Masu Gudun hijira a Niger

Wannan sanarwa na fitowa ne, bayan hare-hare da aka kai kan garin Damasak da ke jihar Borno, wadanda suka yi sanadin raba mutum dubu 65 da muhallansu a cewar kungiyoyin.

Kungiyoyin da ke gudanar da ayyukan jin-kai a arewa maso gabashin Najeriya sun ce mutum miliyan 8.7 na bukatar taimako na gaggawa.

Action Against Hunger da Norwegian Refugees da ke gudanar da ayyukan jin-kai a yankin, sun ce mutanen sun shiga wannan kangi ne, sanadiyyar shekara 10 da aka kwashe ana rikici a yankin.

Darekta Janar na kungiyar Action Against Hunger Jean-Francois Riffaud da babbar Sakatariya a kungiyar Norwegian Refugee Council, Jan Egeland ne suka fitar da wannan sanarawa ta hadin gwiwa.

“A yanzu haka, sama da mutum miliyan daya na adadin wadannan mutane, ba sa samun tallafin ababan more rayuwa, saboda kungiyoyin bada agaji ba sa samun hanyar kai wa ga yankunan da suke.”

Wannan sanarwa na fitowa ne, bayan hare-hare da aka kai kan garin Damasak da ke jihar Borno, wadanda suka yi sanadin raba mutum dubu 65 da muhallansu a cewar kungiyoyin.

Rahotanni sun yi nuni da cewa, mutum 10 aka hallaka a hare-haren.

“Tun daga ranar 10 ga watan Afrilu, kungiyoyi dauke da bindigogi sun kai hari uku a jere akan garin Damasak da kuma ofisoshin kungiyoyin da ke ayyukan jin-kai.”

“Hare-haren sun hada da wanda aka kai kan rumbun adana kayayyakin kungiyar Norwegian Refugee Council da na Action Against Hunger, abin da ya haifa da mummunar barna.”

Kungiyoyin sun kuma yi kira ga gwamnati, da ta tashi tsaye wajen kare rayukan fararen hula tare da samar da cikakken tsaro, saboda hanyoyin da muke bi wajen gudanar da ayyukanmu na jin-kai na ci gaba da tsukewa.”

Sai dai cikin Wata sanarwa da ta fita a ranar Juma'a a shafinsa na Twitter (@HQNigerianArmy) rundunar sojin kasar ta ce ta dakile hare-haren da mayakan na Boko Haram.

Sojojin Najeriya sun kuma musanta rahotanni da ke cewa mayakan sun karbe ikon garin na Damasak.

XS
SM
MD
LG