Domin a cewarsu akwai miliyoyin mutane da ba sa samun maganin makarin wannan cuta wacce ta fi yawa a kasashen masu tasowa musamman a Nahiyar Afrika.
A cewar masanan, hukumomi ba sa maida cikakken hankali wajen yaki da cutar mai haddasa AIDS.
Sai dai kwararru a fannin kiwon lafiya sun ce sun dukufa wajen ganin an samu maganin cutar a duk fadin duniya.
Hajiya Maimuna Muhammed, tsohuwar mai shirya tsare-tsare ce a kungiyar NACA mai yaki da bazuwar cutar a Najeriya.
Jummai Ali ta tambaye ta shin za a yi nasarar kawar da wannan cuta kuwa?
Saurari wannan