A taron manema labarai da ya kira, albarkacin shiga shekarar 2018, Ministan Tsaron kasar Nijar, Kalla Mukhtari, ya bayyana cewa dakarun rundunar hadin gwuiwar kasashen yankin tafkin Chadi sun murkushe kungiyar Boko Haram a kewayen tafkin da sassan jihar Diffa.
Inji Ministan, amma har yanzu akwai 'yan fashi da makami da suke labewa a yankin na Diffa domin yiwa jama'a kwace, lamarin da ya ce za'a kawo karshensa a wannan sabuwar shekarar kamar yadda mayakan Sahel suka fara daidaita al'amura a kan iyakar kasarsa da Mali.
A kan batun girke dakarun kasashen waje cikin Nijar, ministan ya ce ya zuwa yanzu dakarun Amurka da Faransa kawai suke da sansanoni a kasar. Ya ce tarihi ya nuna a duk lokacin da Mali ta yi fama da 'yan tawaye sai Nijar, ta yi fama da nata 'yan tawayen saboda haka hada hannu da wasu dakarun waje domin cimma maslaha shi ne abun da hukumomin Nijar suka sa a gaba.
Dangane da cewa kasar Italiya na shirin kafa nata sansanin a kasar Nijar da zummar yaki da ta'addanci da dakile hanyar da bakin haure ke bi zuwa Turai, ministan ya ce maganar ma ba ta taso ba. Ya ce yanzu ne ma kasashen biyu ke kokarin karfafa huldar diflomasiya tsakaninsu. Yau ne ma kasar Italiya ke shirin bude ofishin jakadancinta a Yamai.
Souley Mummuni Barma na da karin bayani.
Facebook Forum