Mataimakin shugaban Amurka Mike Pence, ya dora laifin karin yaduwar cutar COVID-19 da ake gani a ‘yan kwanakin nan a kasar kan matasa, inda ya zarge su da yin fatali da ka’idojin da aka gindaya na kare yaduwar cutar.
A yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na CBS mai taken “Face The Nation” a ranar Lahadi 28 ga watan Yuni, Pence ya ce “babu haufi” karin gwaje-gwajen da aka yi ne suka kai ga gano karin mutanen da suka harbu da cutar.
Ya kuma kara da cewa “matasa da ke taruka iri-iri ne suke watsi da matakan kariya da gwamnatin tarayya ta shimfida akan yadda za a bi lamarin sannu a hankali wajen maido da harkokin kasuwanci.
Jihohin da suka samu karin mutanen da cutar ta harba sun hada da Florida, Texas da Arizona inda a ranar Juma’a kadai an samu sabbin kamu mutum dubu 40 a kasar
Mataimakin shugaban na Amurka ya soke wata ziyara da ya shirya zai kai a jihohin Florida da Arizona saboda karin adadin mutanen da cutar ta kama a jihohin biyu.
Facebook Forum