Rahotanni suna nuni da cewa, mai baiwa shugaban Amurka mai jiran gado shawara ta fuskar tsaro Michael Flynn, ya tattauna ta woyar tarho sau da dama da jakadan Rasha a Amurka, ranar 29 ga watan Disemba, a ranar da shugaban Amurka Barack Obama, ya kori jakadun Rasha 35, ya azawa kasar takunkumi, a zaman martani na kokarin da hukumomin kasar a Moscow suka yi, na yin shishigi a zaben shugaban Amurka.
Wani babban jami'in Amurka ya fada jiya jumma'a cewa gwamnatin Obama tana sane da kirayen kirayen- tsakanin Flynn da jakadan na Rasha, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya ruwaito.
Amma kakakin shugaban na Amurka mai jiran gado Sean Spicer, ya gayawa manema labarai a jiya jumma'an cewa, Flynn da jakdan na Rasha sun tattauna ne ranar 28 ga watan Disemba, kuma sun yi magana kan shirya tattaunawa tsakanin sabon shugaban na Amurka da tawkaransa na Rasha, bayan da Mr. Trump ya kama aiki, kuma sunyi taya juna murnar kirsimeti.
Ba sabon abu bane tuntubar juna tsakanin gwamnati mai jiran gado da gwamnatocin kasashen waje, amma ganin Flynn yayi magana kuma fiyeda sau daya a ranar da Amurka ta dauki matakin gayya, zai sa a aza ayar tambaya- kan ko Flynn, da jakadan na Rasha, sun tattauna kan martanin da Rashar take shirin dauka.
Wata kafar yada labarai ta wallafa wata makala da ke cewa sai tayu matakin na Flynn ya saba wata dokar Amurka da aka kafa shekaru 200 da suka wuce wacce ta haramtawa Amurkawa kokarin shishshigi ko karkata wata kasar wace, wacce take takaddama da Amurka.
Ahalinda ake ciki kuma shugaban na Amurka mai jiran gado a jiya jumma'a ta shafinsa a dandalin Tweeter, ya sake nanata alwashin da yayi cewa gwamnatins a cikin kwanaki 90 da kama aiki zata bayyana rahoton kan zargin katsalandan daRasha tayi cikin zaben, Amurka, yayi wasu zarge zarge kan bayanai da ba'a tabbatar ba na kaskanci gameda shi, daga nan kuma ya caccaki Hillary Clinton.