A bayan da Argentina ta sha kashi a hannun Chile a wasan karshe na cin kofin Copa America, Lionel Messi yace da alamar dai ba zai taba lashe wani kofi tare da kasarsa ba, don haka ya hakura daga yau.
Lionel Messi Yayi Kuka, Yace Ya Daina Buga Ma Argentina Kwallo Bayan Chile Ta Doke Su
![Lionel Messi yana cire tasa lambar azurfa da aka ba 'yan wasan kasar Argentina, bayan da suka zo na biyu a gasar Copa America. 'Yan Chile suka doke su suka dauki kofin da kuma lambar zinare.](https://gdb.voanews.com/3babdc30-9611-426d-9416-f9a6de9d29c9_w1024_q10_s.jpg)
1
Lionel Messi yana cire tasa lambar azurfa da aka ba 'yan wasan kasar Argentina, bayan da suka zo na biyu a gasar Copa America. 'Yan Chile suka doke su suka dauki kofin da kuma lambar zinare.
![Lionel Messi da sauran 'yan wasan Argentina su na jiran a gudanar da bukin bayar da kofi da lambobi bayan da Chile ta doke su a gasar Copa America.](https://gdb.voanews.com/e2500151-b489-4053-9972-6f4c18d00012_w1024_q10_s.jpg)
2
Lionel Messi da sauran 'yan wasan Argentina su na jiran a gudanar da bukin bayar da kofi da lambobi bayan da Chile ta doke su a gasar Copa America.
![Lionel Messi ya fadi a kasa yana kuka a bayan da Chile ta doke Argentina da ci 4-2 a bugun fenariti a wasan karshe na gasar cin kofin Copa America.](https://gdb.voanews.com/aaadf156-bf98-41a6-af34-bf9321edaa44_w1024_q10_s.jpg)
3
Lionel Messi ya fadi a kasa yana kuka a bayan da Chile ta doke Argentina da ci 4-2 a bugun fenariti a wasan karshe na gasar cin kofin Copa America.
![Wani mai goyon bayan Argentina ya rike baki cike da bakin ciki a bayan da Chile ta doke Argentina.](https://gdb.voanews.com/3247e1f3-b830-4514-a22d-2570c34852e4_w1024_q10_s.jpg)
4
Wani mai goyon bayan Argentina ya rike baki cike da bakin ciki a bayan da Chile ta doke Argentina.