Uwargidar Shugaban Amurka Melania Trump, jiya Jumma'a ta ziyarci gidajen marayu a Kenya - kuma marayun da ta ziyarta sun hada da na mutane da na giwaye, yayin da ta ke gab da kammala ziyarar tsawon mako guda a kasashen Afirka hudu.
Uwargidar Trump ta ratse gidan marayun giwaye a kan hanyarta ta zuwa Gandun Dajin Kasa da ke Nairobi, inda ake kebewa da kuma kare halittu, mai tazarar 'yan kilomitoci a kudu da Nairobi babban birnin na Kenya.
Masu kula da gandun dajin sun gaya ma Uwargidar Trump din irin matakan da Kenya ke daukawa saboda kare giwaye da karkanda, wadanda da yawansu maharba sun karkashe. Hasalima wasu karkandan guda 11 sun mutu a watan Yuli sanadiyyar shan ruwa mai gishiri ainon, bayan da aka kai su wata sabuwar makeba.
Haka zalika, wata hanyar dogo da 'yan China su ka gina a tsawon gundun dajin na janyo takaddama. Hanyar, wacce ta raba gandun dajin gida biyu, an gina ta ne da goyon bayan gwamnati sabanin gargadin da kwararru su ka yi.
Facebook Forum