Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MDD Tace Harin da Amurka Ta Kai Afghanistan Makon Jiya Ya Rutsa da Farar Hula


Janar John Nicholson, kwamandan sojojin Amurka a Afghanistan
Janar John Nicholson, kwamandan sojojin Amurka a Afghanistan

A Afghanistan, ofishin MDD dake can ya fada jiya Lahadi cewa, harin da Amurka ta kai da jiragen yaki a makon jiya, sai tayu ya halaka akalla farar hula 18 galibinsu mata da yara, kamar yadda binciken farko da ofishin yace ya gudanar biyo bayan farmakin.

Farmakin da Amurka da dakarun Afghanistan suka kai a ranakun Alhamis da Jumma'a sun auna mayakan sakai ne a wata gunduma da ake kira Sangin, a lardin Helmand, kamar yadda MDD ta fada.

Ranar Jumma'a, kakakin rundunar mayakan Amurka ya tabbatar da cewa Amurka ta kai farmaki kan wurare da mayakan sakai na Taliban suke a yankin, kuma tana binciken zargin harin ya rutsa da farar hula.

Amma Gwamnan lardin Helmand, da kwamndojin mayakan kasar, duk sun musanta cewa akwai farar hula cikin wadanda harin na Sangin ya rutsa dasu, sun dage cewa an auna harin ne a wurin da mayakan sakai suke, kuma an kashe kusan mayakan Taliban 60 lokacin.

Mayakan sakan masu ikirarin da sunan addinin Islama suke wannan aiki, sun kaddamar da wani gagarumin hari kan yankin na Sangin makonni biyu da suka wuce, suka kama wurare kusa da tsakiyar herlkwatar gundumar.

XS
SM
MD
LG