WASHINGTON D.C. —
Hukumar da ke tsara ayyukan ba da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya OCHA, ta fada a wani rahoto cewa, tashin hankalin da ke karuwa a tsakiyar Mali, na kawo cikas ga ayyukan agajin da ake yi a yankin, lamarin da ka iya jefa rayuwar miliyoyin mutane cikin halin kakanikayi.
A cewar hukumar, adadin mutanen da ke bukatar taimakon, ya karu da kashi 22 cikin 100, wato kusan mutum miliyan hudu.
Rahoton hukumar ya yi nuni da cewa, rayuwar mutum guda cikin kowanne mutum biyar, na dogaro ne da kayayyakin agajin da kasashen duniya ke samarwa.
A cewar kakakin hukumar, Jens Laerk, “da ma idan mutane suka fice daga inda suke yin noman abin da za su ci, ko kuma inda suke kiwon dabbobinsu, wannan na iya zama babbar matsala.”