Majalisar Dinkin Duniya ta shawarci ‘yan siyasar Najeriya da su guji amfani da kalaman batanci da nuna kiyayya da ka iya haifar da husuma a kasar.
Mai wakiltar babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya na musamman kuma shugaban ofishin Majalisar na yankin Sahel a nahiyar Afirka, Mohamed Ibn Chambas ne ya bayyana hakan a Abuja, kamar yadda rahotanni suka nuna.
Chambas ya bayyana hakan ne a wani taron yini guda da hukumar da ke kula da kafafen yada labarai ta NBC ta shirya, wanda ya mayar da hankali kan yadda kafafen yada labarai za su dauki rahotanni a zaben 2019 da ke tafe.
A ranar 16 ga watan Fabrairu Najeriya za ta yi zaben shugaban kasa
Taron ya yi kira ga daukacin ‘yan Najeriya, da su kaucewa duk wani abu da zai iya ta da hankali.
Najeriya na daya daga cikin kasashen da ke fama da batun labaran bogi wadanda kai ya haifar da rikici musamman a wannan lokaci na zabe.
Tun da jimawa hukumomi suke ta yekuwa ga al’umar kasar da ta gujewa yada labaran da ba su da tushe tare da garagadin cewa duk wanda aka samu da laifi zai dandan kudarsa.