Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mazauna Yamai Nijar Sun Yi Zanga-zangar Nuna Fushinsu da Kuncin Rayuwa


Masu Zanga zanga a Yamai babban birnin kasar Nijar
Masu Zanga zanga a Yamai babban birnin kasar Nijar

Mazauna birnin Yamai sun amsa kiran da kungiyoyin da suka shirya zanga zangar suka yi masu inda suka mamaye kusan kilomita biyu kan titin birnin suna kuwa da kirari da nuna bacin ransu a kan halin kuncin rayuwar da suka fada ciki wai saboda sakacin gwamnatin kasar.

Mamman Mustapha Almu na kungiyar WATAP na cikin jigajigaen zanga zangar wanda ya ce garin Yamai ya mutu saboda gwamnati ta kashewa talakawa wurin sana'o'insu.

Inji Almu jama'ar birnin na fuskantar matsaloli da yawa. Babbar kasuwar birnin an rufeta domin ba harkar siyasa ake yi a kasuwar ba, acewarsa. Inji shi kowa ya matsudomin gwamnatin kasar bata tsinana masu komi ba.

Abdullahi Shalare wani masanin harkokin doka ya bayyana cewa matsalolin suna da yawa. Misali, yace babu adalci kuma babu dimokradiya sai karya da makirci.

Zanga zanga a Yamai
Zanga zanga a Yamai

Mutanen da aka rusa shagunan da hukumomin Yamai suka yi ya shafa a watan Agustan wannan shekara su ma sun shiga zanga zangar. Hajiya Gambo wadda ta rasa shagon sayar da abinci tace kasuwanci ya mutu. Da tana da shago inda take dafa tuwo tana sayarwa amma yanzu babu. Tace ta koma 'yar maula.

'Yan adawa da suka zargi shugaba Issoufou Muhammadou da gazawa sun karbi goron gayyata na zuwa zanga zangar daga kungiyoyin fararen hula. 'Yan majalisar dokokin kasa na bangaren adawa suna wurin.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG