A cewar wani ‘dan jam’iyyar APC Aminu Ibrahim Mai Dawa Fage, Idan su kayi haka sun saba yarjejeniya ta dimokaradiyya dama ita yarjejeniyar da shugaba Buhari da jam’iyya suka daukowa al’umman Najeriya, kasancewar ma’aikata sune kashin bayan gwamnati, kuma sune cibiyar dimokaradiyya, idan har ba za’a iya biyansu dubu goma 18 ba to duk gwamnonin da bazasu iya biya ba su sauka daga kan mukamansu.
Suma ‘ya yan jam’iyyar PDP sunyi tsokaci kan wannan al’amari, Mallam Umaru ‘dan Fulani Kawaji wani dattijo ne a cikin jam’iyyar PDP’n Kano. Yace wannan rashin adalci ne kuma akwai kudi, in babu kuma a rage fitar gwamnoni kasashen waje mana.
Baya ga ‘yan siyasa suma kungiyoyin dake bibiyar ayyukan gwamnatoci na bayyana fahimtarsu dangane da wannan yunkuri na gwamnonin Najeriya, na rage albashin ma'aikata, shima jami’in cibiyarsu dake Kano wadda ke bibiyar kasafin kudade na gwamnatotoci Kwamarad Sa’idu Dakata.
Yace wannan ba al’amari bane da ya shafi ‘yan kwadago kadai, idan haka ta tabbata cewa za’a rage albashi ya koma kasa da dubu 18, yana mai tabbatar wa da gwamnatocin jahohi cewa sun gayyaci fada ba ma da ‘yan kwadago kadai ba, har da ‘yan kasuwa da kungiyoyi masu zaman kansu.