Wata kungiyar kula da 'yancin Almajirai da ake kira “Concerned for Almajiris in northern Nigeria” ta koka game da matakan da gwamnonin Arewacin Najeriya suka dauka na mayar da Almajiri zuwa jihohinsu na asali, tana cewa wannan wata hanyace ta tauye hakkin Almajirai.
Shugaban kungiyar Engr. Abdulghafar Onichide ya ce a dokar addinin musulunci ma idan annoba ta bullo a guri shine, to kada a shiga ko a fita, don gudun kada a yada annobar.
Ya kara da cewa a dokar tsarin mulkin Najeriya kowanne dan kasa yana da ‘yancin da zai zauna a ko ina a kasar, "saboda haka wannan mataki da gwamnonin arewacincin Najeriya suka dauka bai dace ba".
Ya ce matakin da gwamnatocin Arewacin Najeriya ya kamata su dauka shi ne raba almajiranci da yawon bara.
Saurari Karin bayani cikin sauti daga Haruna Dauda Biu.
Facebook Forum