Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mayakan 'Yan Tawaye Suna Barin Gabashin Ghouta A Yankin Damascus


Mayakan 'yan tawaye sun taru suna shirin barin yankin Ghouta
Mayakan 'yan tawaye sun taru suna shirin barin yankin Ghouta

Daruruwan mayakan 'yan tawaye ke barin gabashin Ghouta bisa ga yarjejeniyar da Rasha ta shirya da ya sa 'yan tawayen ba ficewa cikin lumana, su da iyalansu

Sama da mayakan yan tawayen Syria 1,500 da iyalansu ne ake kwashesu daga wani gari dake gabashin Ghouta na yankin Damascus da aka yiwa kawanya, yayin da sojojin kasar ke kara dannawa kuma da alamun sun kusa duka sassa dake ciki da kewayen babban birnin kasar.


Motocin safa safa da dama ne suke fitowa da mutane daga garin Harasta, zuwa Idlib, wanda har yanzu yake hannun yan tawaye.


Jami’an yan tawayen sun ce suna sa ran kwashe mutanen zai dauki kwanaki, kuma matakin zai bar wasu tungayen 'yan tawaye guda biyu a gabashin Ghouta.


Kasar Rasha ce ta shiga tsakani aka cimma yarjejeniyar tsakanin yan tawayen Syria da gwamnatin kasar. Yarjejeniyar ta hada da musayar prisinoni kuma tayi daidai da yarjeniyoyin da suka baiwa mayakan yan adawa daman kwashe iyalansu daga yankunan da aka mamayesu cikin lumana.


Rundunar Syria dake samun goyon bayan Rahsa ta kaddamar da hare-hare ta sama da rokoki, har tayi nasarar kwace ikon akan galibin yankuna dake gabashin Ghouta a watan da ya gabata.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG