Gwamnatin kasar Iraki ta ce masu tsattsauran ra'ayi na Daular Islama, sun kashe 'yan wata kabilar Lardin Anbar na kasar sama da 300, ciki har da mata da yara kanana 50, wadanda aka samu gawarwakinsu zube cikin wata rijiya.
An ruwaito wasu ganau na cewa an cigaba da kashe-kashen har zuwa jiya Lahadi, ciki har da 'yan Sunni na kabilar Al-Bu Nimr su 50. Ance tun ranar Asabar aka hallaka wasu 50 su ma.
Bugu da kari, jami'an hukumar kare 'yancin dan adam na Iraki, yayin da su ke bayani jiya Lahadi, sun ce an kama mutane 65 daga cikin 'yan wannan kabilar, bayan da su ka shafe makonni su na fafatawa da 'yan Daular ta Islama kafin makamansu su kare.
Rahotannin kafofin yada labaran Yammacin duniya sun ruwaito wani babban shugaban kabilar mai suna Sheikh Naeem al-Gaoud na cewa ya yi ta kira ga gwamnatin Iraki da ke birnin Bagadaza ta taimaka da karin mayaka da kuma makamai. To amma ya ce babu abin da aka yi.
Gidan Talabijin din Iraki yace Firayim Minista Haider al-Abadi, ya ba da umurnin a kai harin jirgin sama kan wuraren masu tsattsauran ra'ayin dake daura da garin Hit, a matsayin martanin kashe-kashen da su ka yi.