A cikin wani faifan jawabinsa da aka warwatsa a kafofin duniyar gizo a ranar Talatar da ta wuce ne, shugaban kungiyar da ya aiyyana kansa a matsayin shugaban Musulmin yankin, Abu Bakr al-Baghdadi ne yake musu wannan rokon, inda yake kara da nuna musu cewa mutuwarsu wajen kare akidojinsu yafi kima fiyeda ace sun gudu, sun bar fagen dagar.
Wannan sako daga Baghdadi shine na farko tun cikin watan Desimban bara kuma yana zuwa ne makwanni hudu bayanda sojojin Iraqi da na Kurdawa suka kaddamar da yunkurin sake kwato birnin na Mosul dake karkashin ikon IS tun tsawon shekaru biyu.
Kafofin hukumomin liken asirin Amurka sun ce babu wata hujjar yin tambaba a kan ingancin wannan faifan kuma sun tabattarda cewa ba’a dade da daukar sautin sakon ba.