Wannan gargadi yana daga baitocin wakoki da mawaka daga wasu kasashen Afrika ta Yamma masu amfani da truancin Faransa suka rera a wani taron buki a dandalin raya al’adu da nishadi na jami’ar Abdul Mumin ta Niamey a Jamhuriyar Nijer.
Mawakan masu rera wakokin gargadi da suke amfani da salon kahiya sun fadakar da matasa a kan muhimmancin neman ilimi a maimakon jefa rayuwarsu cikin hadari suna ketarawa zuwa kasashen waje ta barauniyar hanya.
Mahalarta bukin wakokin fadakarwar da da ake kira SLAM a takaice sun shirya baitocin wakoki da kalamai masu ratsa jiki suka jan hankalin matasa da suka zo kallo wadanda galibinsu dalibai ne a kan illolin amfani da barauniyar hanya zuwa ci rani.
Hukumar karfafa zaman lafiya ta kasa da hadin gwiwan Kungiyar Tarayyar Turai ne suka dauki dawainiyar shirya wannan taron bukin.