Karar da lauyan madugun ‘yan kungiyar ya shigar dake bukatar rundunar sojin Najeriya, ta fito da Nnamdi Kanu, bata yi wani tasiri ga sojojin ba, domin kuwa shalkwatar tsaro ta bukaci mutane su yi kaffa-kaffa da farfagandar ‘yan kungiyar awaren a dalilin wani faifan bidiyo da ke nuna yadda sojoji suka yiwa gidan madugun dirar mikiya.
Lauyan madugun ‘yan awaren ya bayyana cewa bashi da masaniya ko an kashe Nnamdi Kanu, ko kuma an tafi da shine, dan haka tabayar soji dake atisayen operation Python dance, bai taso ba a cewar kakakin rundunar sojin Najeriya, birgediya janar Sani Usman Kuka Sheka.
Da yake bayani, janar kuka sheka ya kara da cewa ko shekarar data gabata dakarun sun gudanar da irin wannan atisaye kuma babu abin da ya faru dan haka duk farfaganda ce kawai, ko kwanakin baya ma kanen madugun ‘yan awaren ya ce a boye suke kuma baza su bayyana inda suke ba.
A bangaren masana harkokin shari’a kuma, ko mai zai faru idan lokacin komawarsa kotu yayi kuma ba’a zo da shi ba? Tamabayar da wakilin sashen Hausa na muryar Amurka Nasiru Adamu Elhikaya, ya yiwa lauya mai zaman kansa a Abuja, Barista Zubairu Namama, wanda ya bayyana cewa kotu na iya rike wadanda aka ba belin madugun ‘yan awaren kokuma ta rike abinda suka bada a matsayin jingina.
Jami'an tsaron Najeriya, sun bayyana matsayar su dangane da madugun a matsayin ya buya ne.
Domin Karin bayani, saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El-hikaya.
Facebook Forum