Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sami Barkewar Annobar Kyandar Biri A Jihar Bayelsa


An sami labarin barkewar annobar cutar kyandar Biri a jihar Bayelsa da ke yankin Niger Delta a tarayyar Najeriya.

Ma’aikatar lafiya ta jihar ta tabbatar da afkuwar barkewar annobar cutar Biri a jihar Bayelsa, kuma ta ce an kebe kimanin mutane goma da suka kamu da cutar kana ana ci gaba da neman wasu da dama da ake kyautata aton sun kamu da wannan cuta domin a killace su wuri daya.

Hukumar kula da lafiya ta jihar ta aika da amfarin kwayar cutar ga sashin bincike da gwaje gwaje na hukumar lafiya ta duniya dake kasar Senegal domin tantancewa yayin da sakamakon gwajin zai tabbatar ko annoba ce.

Rahotanni sun bayyana cewa daya daga cikin mutane goma da suka kamu da cutar likita ne, kuma yanzu haka ana neman mutane arba’in da tara domin a kebe su, wasu rahotanni kuma sun bayyana cewa akalla mutane goma sun riga mugidan gaskiya a sakamakon kamuwa da cutar.

Mr Daniel Maxing, shine kwamishinan ma’aikatar watsa labaru a jihar ta Bayelsa, ya sami zantawa da wakilin sashen Hausa na Muryar Amurka, Abubakar Lamido Sakkwato, ta wayar salula kuma ya bayyana masa cewar akalla mutane goma na kebe a yanzu haka domin kaucewa yaduwar cutar.

Jama’a da dama a fadin jihar sun bayyana halin da ake ciki a matsayin masifar data shafi kowa da kuma yin kira ga gwamnati data gaggauta shawo kan lamarin. A halin da ake ciki dai jama’a da dama basa musabaha da juna kamar yadda aka saba domin gujewa kamuwa da wannan cuta.

Cutar kyandar Biri dai ta samo asali ne daga Birai da kuma sauran dabbobi da ake mu’amulla da su irin su barewa.

Ga rahoton Lamido Abubakar Sakkwato daga Fatakwal.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:05 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG