Gwamnan jihar Neja Abubakar Sani Bello, a lokacin da ya gana da wasu daruruwan ‘yan banga a karamar hukumar Kontagora, ya bayyana cewa ya zama dole a gode musu saboda aikin da su ke yi na tsare gidaje, da al’umma, su na kuma taimaka wa ‘yan sanda da sojoji. Ya kara da cewa duk abinda ya dace a yi don a taimaka musu da kayan aiki za a yi Insha Allahu,
"Akwai ‘yan uwanmu da yawa da suka rasa rayukansu, gwamnati za ta duba yadda za a taimaka wa iyalansu amma abinda ya fi muhimmanci a ciki shi ne, duk wanda ya rasa ransa, gwamnati za ta dauki nauyin kudin makarantar ‘yan’yansa," a cewar gwamnan.
Lamarin ‘yan bindiga a jihar Neja dai na ci gaba da kara ta’azzara, kamar yadda wani mazaunin karamar hukumar Mashegu ya shaida, ya na mai cewa 'yan bindiga sun kama wasu wurare a cikin jihar Neja sun kuma kori manoma da mazauna kauyukan.
Wannan al’amari dai ya sa a yanzu haka manyan jami’an gwamnatin jihar Neja yin damarar sa kayan 'yan banga domin tunkarar ‘yan bindigar. Kwamishinan ma’aikatar kula da harkokin kananan hukumomi da masarautu na jihar Neja, Barista Abdulmalik Sarkindaji na daya daga cikin waddanda suka saka kayan ‘yan bangar.
"Harkar tsaro aiki ne na duk wani mai hankali ba na ‘yan banga ba ne kadai. Ya kara da cewa idan kwamishina zai sa kayan 'yan banga don neman miyagu, to kai da ka ke gida me zai hana ka yi? a cewar Abdulmalik.
Daya daga cikin shugabannin ‘yan bangan Alhaji Aliyu Makiga, ya nuna gamsuwa da tallafin da gwamnatin ta ce za ta basu, ya kuma ce su na bukatar kayan aiki domin tunkarar wadannan ‘yan bindiga da ko a makon jiya sai da suka hallaka wasu sojojinn Najeriya guda shida tare da wasu ‘yan bangan guda biyu a jihar Neja.
Saurari cikakken rahoton Mustapha Nasiru Batsari.