Rangadin dai ya fara ne a jihar Sokoto, inda ‘yan kasuwar suka hadu da manoma daga jihohin Kebbi da Zamfara suka tattauna matsalolin.
Aiyukan ta'addanci da suka hana manoma zuwa gonakin su, da yawan satar mutane akan hanya na daga cikin manyan matsalolin da suka addabi manoma da ‘yan kasuwa, har ma da shafar harkar sufurin kayan gwari zuwa kudancin Najeriya.
Haka kuma, kisan da aka yiwa manoma a jihar Borno ya kara jefa tsoro cikin zukatan manoma, ga kuma ambaliyar ruwa da aka samu lokacin damuna a arewacin Najeriya, wadda ta kara hana yin noman kayayyaki balle ta kai ga sufurin su zuwa Kudu.
Aliyu Mai Tasamu Isa, shine shugaban kungiyar masu noma da sayar da albasa ta Najeriya ya ce, ko bayan wadannan matsalolin na rashin tsaro akwai wasu kalubale dake tarnaki ga yawaitar kayan har a kai su wani wuri.
Alhaji Dauda Sulaiman jigo, babban manomi ne kuma mai kasuwancin Tattasai da Tarugu ya ce akwai bukatar hukumomi su mayar da hankali ga matsalolin da ke tarnaki ga manoman kayan gwari saboda muhimmancin da suke da shi.
Jihohin arewacin Najeriya, suna sahun gaba wajen samar da kayan gwari da ake amfani da su a Najeriya da ma wasu kasashen Afirka.
Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Muhammad Nasir.