Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matsalar Fasakwauri Ce Take Haifar Da Hauhawar Farashin Shinkafa - Ministar Kudi


Ministar Kudin Najeriya Zainab Shamsuna Ahmed (Instagram/ Zainab Shamsuna
Ministar Kudin Najeriya Zainab Shamsuna Ahmed (Instagram/ Zainab Shamsuna

Ministar kudi, kasafi da tsare-tsare ta kasa, Zainab Shamsuna Ahmed, ta bayyana cewa fasakwauri ne ke haddasa tashin farashin shinkafa a Najeriya.

Ministar ta bayyana hakan ne a cikin shirin siyasa a yau na gidan talabijan na Channels, inda ta ce ayyukan fasakwauri na yi mumunan tasiri kan kasuwanci da kuma cutar da 'yan kasar lamarin da ta danganta da abin takaici sakamakon yadda wasu gurbatattun mutane ke shigowa da kayayyaki da gwamnati ta armata cikin kasa.

Haka kuma, ministar kudi ta ce akwai ‘yan Najeriya marasa kishin kasa da ke shigowa da shinkafa mara inganci, wasu ma ba zasu ciyu ba kuma don neman kazamar riba miyagun ke kawo su cikin gida a zuba a kasuwa.

Zainab ta kuma nanata kokarin gwamnatin tarayya na yaki da ayyukan fasakwauri, inda ta bayyana cewa hukumar hana fasa kwauri ta kasa wato NCS, ‘yan sanda, jami’an tsaro na farin kaya wato DSS da sauran su na hada gwiwar domin kawar da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa.

A game da bukatar sabbin rancen da majalisun kasar ta amince gwamnatin tarayya karbo na baya-bayan nan, Zainab ta ce gwamnati ta kirkiro da tsarin kula da basussuka na matsakaicin lokaci, inda ta ce ba ta hanyar neman umarni daga kotu wato fiat ne ne gwamnati ke karbar bashin ba.

Lamarin da ta ce tun farkon shekarar 2021 da mu ke ciki ne gwamnatin tarayya ta shigar da bukatar neman rancen da majalisun kasar suka amince da shi ba sabon bukata ba ce.

Idan ana iya tunawa, a watan Mayun ne shugaba Muhammadu Buhari ya mika bukatar karbo rance ga majalisar dattawar kasar sannan suka amince a karbo a baya-bayan nan.

Shirin neman rance ko lamuni daga kasashen waje na shekarar 2018 zuwa 2020 ya kunshi bukatun neman amincewar majalisa da kudin a jimlace suka kai dala biliyan 36 da miliyan 800, Yuro miliyan 910, da bangaren tallafi na dala miliyan 10.

Tun daga shekarar 2018 zuwa yau ne 'yan majalisar suka fara amincewa da bukatun neman rance inda suka amince da karbo dala biliyan 8 da miliyan 300 da kuma Yuro miliyan 490 a watan Yuli, daga baya suka kuma amince da gwamnati ta karbo dala biliyan 6 da miliyan 100 a cikin wannan watan da mu ke ciki.

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG