Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Da Gaske Babban Bankin Najeriya Ya Raba Biliyoyi Ga Wasu Manyan Kasa?


Abubakar Malami, Ministan Shari'a a Najeriya
Abubakar Malami, Ministan Shari'a a Najeriya

Minista Shari'a a Najeriya Abubakar Malami, ya musanta rahotanni da ke cewa Babban Bankin kasar na CBN, ya rabawa wasu mutane da kamfanoni biliyoyin kudade ba bisa ka'ida ba.

Rahotanni sun nuna cewa wasu manyan jami'an fadar gwamnatin tarayyar Najeriya sun tilastawa bankin na CBN, ya rabawa wasu kamfanoni da wasu mutane naira biliyan 133.

Amma Malami, ya shaida wa Muryar Amurka cewa, "babu kanshin gaskiya a wannan labarin."

A cewarsa, matakin na tilastawa "yana iya faruwa ne ta fannoni biyu, ko dai da karfin dambe, ko kuma amfani da karfin iko na karfin mulki, amma babu inda aka yi amfani da ko daya."

Baya ga shi Ministan Shari'a, rahotannin sun ambato Shugaban Ma’aikata na fadar Shugaban Kasa, Farfesa Ibrahim Gambari da Ministar kudi Zainab Ahmad Shamsuna, a matsayin sauran jami'an gwamnatin da suka matsa sai an rasa wadannan kudade da wasu daidaikun mutane, duk da rashin amincewar Shugaba Muhammadu Buhari, da gwamnonin kasar.

Karin bayani akan: Babban Bankin Najeriya, Abubakar Malami​, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

Ministar Kudi Zainab Ahmed
Ministar Kudi Zainab Ahmed

Malami ya kara da cewa, wannan wani yunkuri ne na wasu da ke son amfani da wata dama don cin zarafin ofishin Atoni janar da na mai taimaka wa Shugaban Kasa a Bangaren Ma'aikata, da kuma ofishin Ministar kudi.

Duk wanda aka biya shi kudi a hukumance to za a tarar cewar ya yi aikin da ya cancanci a biya shi wadannan kudaden, kuma babu inda aka yi aiki mai kama da alfarma ga wani.

Malami ya kara da cewa idan kuwa akwai shaidu da ake da su na wadanda za su nuna tilasta biyan kudi, sai a gabatar da su ga jami'an da hakki ya rataya a wuyansu.

Jaridar yanar gizo ta Moonlightnews ta ruwaito wata majiyar da ta bayyana mata cewa, "Malami, Ned Nwoko da Gambari tuni su ka samu nasu kason cikin kudin.

Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Abdul'aziz Yari
Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Abdul'aziz Yari

"Sannan Nwoko ya sayi jirgi da farko kuma lokacin da jirgin ya yi hatsari, sai ya sayi na biyu kuma ya auri karamar yarinya (Regina Daniel). Da sauran kudin, ya sayi manyan gidaje a Abuja sannan ya samu karayar arziki na wani dan lokaci," a cewar jaridar ta Moonlightnews.

Kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito, yawan wadanda suka ci gajiyar kudin ya bayyana sunayen mutane shida da kuma hukumomin da ake binsu jimillar $ 418,953,670.59, kusan naira N159 biliyan.

Farfesa Ibrahim Gambar
Farfesa Ibrahim Gambar

A cewar Moonlightnews, "wadanda suka ci gajiyar sun hada da wani tsohon dan Majalisar Wakilai, dan siyasa kuma lauya, Ned Nwoko, wanda ke gabatar da bukatar dala 142,028,941 (kimanin Naira biliyan 54) ta hanyar hukuncin amincewa da ya samu daga Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a karar, wacce aka sanya wa lamba FHC / ABJ / CS / 148 / 2017.

Masu cin moriyar uku sun gabatar da bukatar dala 143,463,577.76 (kimanin Naira biliyan 54.6) ta hanyar hukuncin Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya (FCT) a karar da ke lamba FCT / HC / CV / 2129/2014 sune: Riok Nigeria Ltd, Orji Nwafor Orizu, da Olaitan Bello.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG