Yayin da kasashen duniya ke bukukuwan ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe a matsayin ranar yaki da cin hanci, hukumar yaki da cin hanci a Jamhuriyar Nijar ta bayyana dalilan siyasa a matsayin wata hanyar da ke kara dagula yaki da wannan matsala.
Shugaban hukumar yaki da cin hanci a kasar, Mai Shari’a Abdurrahman Gousman, ya ce, ma’aikatun gwamnati suke kan gaba wajen yawan karbar cin hanci.
Ya kara da cewa duk da irin nasororin da ake samu, har yanzu “akwai sauran rina a kaba.”
Baya ga ma’aikatun gwamnati a cewar Gousman, jam’iyun siyasa su ne na biyu a sahun karbar cin hanci sai kuma kungiyoyin fararen hula.
Mataimakin hukumar, Salisu Ubandoma, ya ce yaki da cin haci da rashawa, wani lamari ne da ke bukatar hadin kan kowa da kowa.
“A da, inda ba a samun cin hanci shi ne cikin makaranta ko kuma fannin likita, (Asibiti) to amma yau matsalar ta zama gama gari, ko in aka je akwai cin hanci da rashawa.” Inji Ubandoma, a lokacin wata hira da ya yi da Sashen Hausa na Muryar Amurka.
Facebook Forum