An kashe akalla mutane uku a wani rikicin daya barke tsakanin Fulani makiyaya da kabilar Gwarawa manoma a jihar Nija.
Rikicin ya barke ne a daren Litinin a kauyen Lau dake yankin karamar hukumar Shiroro. Hakimin yankin Alhaji Tanko Baba Kuta ya shedawa sashen Hausa cewa rikicin ya tilastawa daruruwan Gwarawa tserewa daga gidajensu.
Yace Fulani sun kori mutanen su daga gidajensu. Yanzu haka mutanen sun fake a wata makaranta. Hakimin yace mutanen dake gudun hijira sun kai fiye da dari biyu.
Mataimakin shugaban kungiyar Miyetti Allah ta kasa, Alhaji Husseni Botso yana daya daga cikin wadanda ke shiga tsakani domin sasanta tashin hankalin. Yace karamin magana ce ta zama baba. Alhaji Hussein yace rikicin ya barke ne a saboda rashin hakuri. Ya kuma musunta cewa Fulani sun hana Gwarawa komawa matsugunin su.
Rikicin Fulani makiyaya da manoma yana kara ta'azara a jihar Nija, domin ko a ranar Lahadi an yi wani tashin hankali tsakanin Fulani da wasu 'yan banga a yankin Lambatta dake karamar hukumar Gurara. Rikici na ranar Lahadi yayi sanadin mutuwar mutane hudu.
Rundunar 'yan sandan jihar Nija ta tabbatar da aukuwar lamarin Mai magana da yawun yan sanda Bala El Kana yace 'yan sanda suna tsare da wasu 'yan banga guda uku akan rikicin na Lambatta
Haka kuma yace rundunar 'yan sanda tana kuma gudanar da bincike akan rikicin daya auku a karamar hukumar Shiroro. Suna kuma ganawa da shugabanin bangarorin domin fadakar dasu muhimmancin zaman lafiya.