WASHINGTON, DC —
Rahotani daga garin kala balge a arewacin Borno na nuni da cewa wasu mahara da aka yi kiyasi su adadinsu ya kai dari biyu su gamu da ajalinsu lokaci da suke kokarin kai hari kan mutane garin kala balge a jihar Borno.
Wannan kuka kura da aka ce mazauna garin sukayi masamman matasan da ake kira sibiliyan JTF baya rasa nasaba da hare-haren da ‘yan bindiga ke kaiwa kan jama’a.
Sun samu nasaran kame goma daga cikin ‘yan bindigar da ransu,inda suka karbe makamai da motoci biyu da kuma wata motar yaki mai dauke da fentin sojojin Najeriya.
Hukumomin tsaro a jihar Borno sun tabbatar da abkuwar lamari amma bazuyi wani kari haske game da batun ba.
Shugaban matasa ‘yan kungiyar sibiliyan JTF Ba Lawan yace“ kwarai yaran su,sunyi nasara su karbe makamai da motoci,kuma sun samu labari cewa maharani na kokarin sake kai wani sabon hari.