Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasa Sun Yi Wa Buhari Tuni Kan Nadin Mukamai


Aminu Muntari Malunfashi
Aminu Muntari Malunfashi

A shirinmu na Matasa Da Siyasa, wakiliyar Dandalin VOA, ta yi hira da Aminu Muntari Malunfashi dan Kungiyar Buhari "For Change Next Level," wato wadanda suka yi fafatukar tabbatar da shugaba ya zarce.

Matashin ya ce sun yi kokarin tabbatar da zarcewar gwamnati amma suna tunawa shugaba Buhari cewar kar ya manta da matasa.

Ya kara da cewa sha'anin harkar siyasa da matasa na neman gyara tun da ba kowane matashi ne ke da damar iya wa ba.

Amma ya kara da cewa sun sani tafiya ta mulki dole ne ta hada da kowa daga matasan har masu shekaru.

Ya ce ba’a sakarwa matasa damar damawa da su ba, ko a yanzu matasa ba su fi kaso 30 cikin 100 cikin mulki dimokradiya da ke wakana a yanzu ba, duk da cewar sai da su ne ake kafa kowacce irin gwamnati.

Akan tambayar cewa wadanda suka yi wa shugaba Buhari taimako, ya kan manta da su, Aminu ya ce ba haka zancen yake ba, duk da cewar sun yi masa fafatuka, an yi alkawarurruka da ba'a cika ba, amma ya ce suna yi masa uzuri kasancewar hadaka da wasu jam’iyyu da aka yi.

A kan haka ne suke tuni da cewar ko anan jiharsu, akwai wadanda suke ganin idan aka ba su dama lallai za su kawo ci gaba ga kasa ba ki daya, tunda, ya amince da irin fafatukar da suka yi masa a harka ta siyasarsa tun daga tushe kuma tun kafin a kafa mulkin farko ga na biyu nan suna dako.

Ya ce akwai matasan da ya kamata a ce an rungume su a ganin su ma sun ba da gudunmuwar da kudirorin ci gaban dimokradiyya.

Saurari cikakkiyar hirar da wakiliyar Dandalin VOA, Baraka Bashir ta yi da Aminu Muntari Malumfashi:

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:00 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG