Matakin jingine zaben ‘yan Nijer mazauna ketare da hukumar zaben kasar ta bayyana shirin dauka sanadiyyar annobar COVID-19, ya janyo ce-ce-ku-ce da suka daga wadanda ke wakiltar ‘yan Nijer mazauna ketare a majalisar dokokin kasa.
Wakilan sun ce ba za su yarda da dukkan wani yunkurin hana masu morar ‘yancinsu na ‘yan kasa ba.
Shugaban hukumar zabe Me Issaka Souna da yake bayani a wani taron ‘yan siyasa dangane da inda aka kwana game da tsare-tsaren zaben da ake saran gudanarwa a karshen shekarar 2020, ya ce, annobar coronavirus da ake fama da ita ba za ta bari ‘yan Nijer mazauna kasashen waje su yi zabe ba a wannan karon,.
Sai dai ra’ayoyi sun sha bamban a tsakanin ‘yan majalisar na "Diaspora" domin a ra’ayin Hon. Alfari Abbas hujjar da hukumar zabe ta CENI ta bayar wajen daukan wannan mataki bai kai matsayin da za a yi mata uzuri ba.
Kundin tsarin mulkin Nijer ya baiwa ‘yan kasar na ciki da waje matsayin guda a gaban dokar zabe, saboda haka Hon. Moumouni Issa Djibo ya ce, muddinn hukumar CENI ta yi biris da zaben ‘yan Diaspora, to za su bi hanyoyin da doka ta yi tanadi domin neman hakkinsu.
Shirya zaben cike gurbe a kasashen da annobar COIVD-19 ta hana a shirya zaben Nijer akan lokaci itace hanya mafi a’ala wajen kaucewa taka doka inji Hon. Alfari Abass.
Saurari Karin bayani cikin sauti daga Souley Moumouni Barma.
Facebook Forum