Daruruwan mutane ne aka kashe a fadan kabilancin da ake ci gaba da yi a arewa maso gabashin Sudan ta Kudu cikin makonni biyu da suka gabata, a cewar wakilin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya a kasashen Afirka.
Shugaban shirin samar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ta Kudu da ake kira UNMISS a takaice, David Shearer, ya fada wa Muryar Amurka cewa tashin hankalin da ake yi a karamar hukumar mulkin Pibor ya karu matuka idan aka kwatanta da shekaru biyu da suka gabata.
Ya ce yana fatan yarjejeniyar nada gwamnonin jihohi da jam’iyyun siyasa na Sudan ta kudu suka cimma a ranar Larabar da ta gabata za ta taimaka wajen samar da tsarin girma a hukumace ta kuma rage aukuwar irin wadannan rikice-rikicen.
"Akwai guraban mukaman da ba a cike ba saboda a wadannan yankunan, musamman a jihar Jonglei, ba a cimma yarjejeniya kan tsarin shugabanci ba. Ta yiwu akwai yarjejeniyar da gwamnati da jam’iyyun adawa suka cimma akan raba mukaman gwamnonin a jihohi 10. Idan haka lamarin ya ke, to yana da muhimmanci saboda hakan na nufin za mu samu akalla hukuma a wuraren,” abin da Shearer ya fada wa Sashen Sudan ta Kudu na Muryar Amurka kenan a wata hira ta musamman a ranar Laraba 17 ga watan Yuni.
Facebook Forum