Hukumomin kiwon lafiya a Jamhuriyar Nijar sun tabbatar da cewa suna daukan matakan dakile yaduwar kwayar cutar Coronavirus, musamman a filin jirgin saman Diori Hamani na Yamai.
An dai fi samun cunkoson jama'a a wannan filin jirgi da ke ganin matafiya daga sassan na duniya, musamman ma daga China.
Hukumomin sun kuma sanar da cewa sun tsaurara matakai akan iyakokin Nijar da Najeriya sakamakon annobar cutar "Lassar Fever" da ta barke a wasu jihohin Arewa.
A taron manema labaran da ya kira, shugaban ma’aikatar yaki da yaduwar cututtuka da annoba, Dr. Adamou Moustapha ya bayyana cewa har yanzu ba a samu labarin bullar kwayar cutar Coronavirus a Nijar ba duk da cewar cuta ce da ke saurin yaduwa.
Manyan Jami’an ma’aikatar lafiya ta kasa tare da hadin gwiwar takwarorinsu na hukumar lafiya ta Duniya OMS ko WHO, sun kai ziyarar aiki a yammacin jiya Litinin a filin jirgin saman na Diori Hamani.
Ziyarar ta su, ta kunshi tabbatar da an tsaurara matakan riga-kafi a ci gaba da neman hanyoyin kare jama’a daga wannan annoba da aka bayyana cewa ta kashe gomman mutane a kasar China.
Annobar cutar Lassar Fever da ta barke a Najeriya wani abu ne kuma da ma’aikatar lafiyar Jamhuriyar Nijar ke dauka da matukar mahimmanci.
Abin da kenan ya sa aka tsaurara matakan zuba ido akan matafiya a iyakokin kasashen biyu, inji Dr. Adamou Moustapha.
Kungiyoyi masu zaman kansu a nasu bangare, na cewa ya zama wajibi tun yanzu a maida hankali wajen ayyukan waye kan jama’a.
A saurari rahoto cikin sauti daga birnin Yamai.
Facebook Forum