Mataimakiyar Shugaban Amurka Kamala Harris Ta Ziyarci Wata Cibiyar Fasahar Aikin Matasa A Ghana
Mataimakiyar shugaban Amurka Harris da ta kai ziyara Ghana, a kokarinta na yin hulda ta kai tsaye da matasa da kuma nuna muhimmancin fasahar fannin kirkire-kirkire a fadin nahiyar, Harris ta ziyarci cibiyar Vibrate Space, wani gidan wasan kwaikwayo da matasa masu fasaha suke a Freedom Skatepark.