Mataimakin shugaban kasar ya kai ziyara a Koriya ta Kudu a shirin ziyararsa ta kasashe hudu don kara karfafa alakar da ke tsakanin Amurka da kawayenta da kuma nuna jajircewar ta ga yankin da ake dari dari dashi gami da gina tallafin kasa da kasa domin kara matsawa gwamnatin Kim Jon Un lamba don dakatar da shirye shiryen gwajin makamin kare dangi da kuma na makami mai linzami samfurin Ballistic.
A daya bangaren kuma Alkali a Koriya ta Kudu ya tuhumi tsohuwar shugabar kasar Koriya ta Kudun da aka hambarar daga kan mulki Park Geun-hye da laifin karbar cin hanci lamarin da ya kaiga tsigeta.
Ofishin kotun ya tuhume ta ne a yau Litinin inda aka maida shari’arta zuwa Kotun Munanan Laifuka.
Munanan laifukan da ake tuhumar Park da su sun hada da rikicin da ya jawo ta rasa mukaminta. An zargeta da hada kai da wata tsohuwar kawarta Choi Soon-sil da damfarar wasu kamfanoni su bada gudummawa ta fiye da Dalar Amurka miliyan $69 zuwa wasu Gidauniyoyi guda biyu na jabu.
Facebook Forum