A yau ne da safe a garin Tirmini aka gudanar da sallar mata na Niger, an samu halartar mata da dama, maudu'in na bana shi ne inganta ilimin mata don samun dogaro mai dorewa a bangaren matan.
Maudu’in na bana shine “Inganta Ilimin Mata domin tabbatar da Dogaro da kai mai dorewa a fanin tattalin arziki wa mata”.
Mataimakiyar darakatar kyautata rayuwar mata da yara kanana ta Damagaram Madam Sani Hajiya Magajiya, ta bayyana dalilin wanna maudu’in nasu shine bias kare jahilci wanda yake nufin makarantar domin kawar da jahilci.
Ta kara da cewa baya mutun ya samu ilimi tilas ne mutun ya samu aikin yi, tana mai cewa matsaloli yanzu a karkara sai shukura domin kusan koina akwai inji na yin nika.
Sai dai yayinda wakiliyar muryar Amurka Tamar Abari, ta ziyarci wasu kyauyuka mata sunce su basu san cewa akwai wata Sallar mat aba sun kuma koka da rashin abinci da ruwan sha.
Facebook Forum